Fadar Shugaban Najeriya ta ce babu adalci idan aka zargi cewa shugaba Muhamamdu Buhari na jan kafa wajen sanya hannu a kan kudirin dokar zaɓe ta 2022.
Hakan na zuwa ne bayan ƙungiyoyin fararen hula da wasu masu ruwa da tsaki sun zargi shugaban da jan ƙafa wajen sa hannu a kan dokar duk da ɗumbin muhimmancinta.
Mai magana da yawun Shugaban ƙasar, Mallam Garba Shehu ya ce masu waɗannan zarge-zarge ba su yi wa shugaban adalci ba.
Sannan ya sake sake jadada cewa a ranar Juma’a 26 ga watan Fabarairu shugaba Buhari zai sa hannu kan ƙudurin dokar zaɓen da ake ce-ce-ku-ce a kanta.