Kotu ta ɗaure mutumin da ya ƙara aure ba tare da amincewar uwargidansa ba

Date:

 

Wata kotu a Pakistan ta ɗaure wani mutum wata shida a gidan yari saboda ya ƙara aure ba tare da amincewar matarsa ta farko ba.

Kotun da ke Lahore ta yi watsi da ikirarin mutumin mai suna Saqib cewa addininsa ya ba shi ƴanci a matsayinsa na musulmi.

BBC Hausa ta rawaito matarsa Ayesha Bibi, ta yi nasara a kotun, bayan ta yi iƙirarin cewa ƙarin auren ba tare da amincewarta ba ya saɓa wa dokar iyali ta Pakistan.

Kotun ta ci tarar mijin dala dubu biyu.

Masu fafutikar kare haƙƙin mata, sun ce hukuncin zai karya guiwar mazan da ke da niyyar ƙarin aure, kuma zai buɗe wa mata ƙofar kai mazajensu kotu.

A Pakistan maza na auren fiye da mata ɗaya, amma dole sai namiji ya nemi amincewar matarsa ta farko kafin ya auri ta biyu.

Yanzu Saqib na da damar ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun.

An daɗe majalisar harakokin addinin Islama a Pakistan na ƙalubalantar dokar iyali ta Pakistan tare da ba gwamnati shawarwari da suka shafi harakokin addini.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...