Da dumi-dumi: APC ta Amince Shugaban Jam’iyyar ya fito daga Shiyyar Arewa

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida
 Jam’iyyar APC mai mulkin Nigeria ta tsayar da Amince ta fitar da shugabanta daga yankin Arewacin Najeriya a Babban zaben da zata gudanar.
 Gwamna Nasiru El-Rufai na Kaduna da Atiku Bagudu na Kebbi, ne suka bayyana hakan a lokacin taron manema labarai da suka gudanar bayan ganawar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja.
 El-Rufai ya ce jam’iyyar ta amince da sauya mukaman Shugabannin jam’iyyar Musamman na kwamitin kolin jam’iyyar na kasa (NWC) tsakanin Arewa da Kudancin kasar nan a babban taron jam’iyyar wanda za ta gudanar a ranar 26 ga Maris 2022.
 Idan dai za a iya cewa, mukamin shugaban jam’iyyar na kasa wanda tsohon Gwamna John Odigie-Oyegun da Adams Oshiomhole na Jihar Edo Suka rike sun fito ne daga Kudu to shi ne zai koma Arewa.
 El-Rufai ya ce, “Mun amince da tsarin shiyya-shiyya na shiyyoyin siyasa guda shida, kuma mun yi musanya da su. Shiyyoyin Arewa za su dauki mukaman da shiyyar Kudu Suka rike shekaru takwas da suka wuce.
 “Don haka, tsari ne mai sauqi qwarai, daidaito da adalci.  Yanzu za mu koma mu tuntuba a matakin shiyya, mu duba mukaman da ake da su kuma za a fara shirye-shiryen taron da ka’in da na’in.  Don haka da yardar Allah ranar 26 ga Maris za mu yi babban taron mu na kasa.”inji El-Rufa’i
  taron dai ya gudana ne a zauren majalisar zartarwa ta Kasa dake fadar shugaban kasa a Abuja ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da gwamnoni 19 da suka hada da na Yobe, Kano, Kogi, Ekiti, Nasarawa, Kwara, Ebonyi, Jigawa, Lagos, Imo.  Ogun, Borno, Niger, Gombe, Osun, Kebbi, Plateau, da kuma mataimakin gwamnan jihar Anambra wanda ya baro jam’iyyar APGA zuwa APC a bara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kwamitin PTA na Kano ya dauki matakan hana ragewa dalibai hanya bayan taso su daga makaranta

DAGA ABDULHAMID ISAH Shugaban Kwamitin Iyayen yara da Malamai na...

Fada daba: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf – Daga Zainab Nasir Ahmad

Daga Zainab Nasir Ahmad Mai Girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Abba...

RATTAWU ta Kano ta taya Abbas Ibrahim Murnar sabon mukamin da NUJ ta ba shi

Kungiyar ma'aikatan Radio da Talabijin ta kasa reshen jihar...

NUJ ta kasa ta baiwa Abbas Ibrahim sabon mukami

Daga Aliyu Abdullahi Danbala   Kungiyar yan Jarida ta Nigeria ta...