KARANCIN KUDI GA MASU SHIRYA FILM YA JANYO YAKIN CACAR BAKA A KANNYWOOD – SANI M GARKO

Date:

Daga Sani Magaji Garko.

Masana’antar shirya fina-finan Hausa dake da shalkwata a jihar Kano dake Arewacin Nigeria ta fada cikin yakin cacar baka bayan tattaunawar da Sashen Hausa na BBC cikin shirin (Daga bakin Mai Ita) yayi da wata tsohuwar jaruma da aka fi Sani da Ladin Cima Haruna inda a cikin tattaunawar ta ce ana bata dubu biyu (2,000) ko dubu uku (3,000) ta yi “film”.

Fadar ana bata dubu biyun ko ukun ce ta harzuka wasu daga cikin masu shirya fina-finan Hausa dama jarumai lamarin da har suka kasa jurewa, sai da sukayi martani a shafukan sada zumunta na zamani.

Daga cikin wadanda hakan baiyi wa dadi ba akwai su Sarki kamar yadda suke kiransa ko Kuma Ali Nuhu da kuma sannen Mai shirya fina-finai Falalu A. Dorayi wanda suke ganin kamar Ladin cima ta Fadi haka bai dace ba, domin hakan kamar zubar da kimar masana’antar ne a idon duniya ko kuma wani wani Abu Mai kama da haka wanda hakan ne ma yasa suka fito karara tare da yin Allah wadai ko inkari akan hakan.

To amma ga wani Sarkin a dai masana’antar ta Kannywood a wannan karon Sarkin Waka Naziru M. Ahmad abin da ladin cima ta fada Babu komai sai tsagwaron gaskiya.

Hakan yasa shima ya bude nasa shafin tare da nadar faifen bidiyo inda a cikin sa yake inkarin akan abun da Ali da Falalu ke fada, harma yake cewa suna da masaniya cewa “abinda da ladin ta fada Gaskiya ne domin wasu daga cikin dattawan Yan film ma idan sunyi ce musu ake suje zaa kira su, wasu ma sai sun bada kudin su a saka su, kai wasu ma sai anyi abin da bai kamata ba a saka su “(ko ki ba da kudi ko ki bada kanki)” kamar yadda ya fada a cikin faifen.

Wannan yar tsama ko fadi in fada ce ta jawo cece-kuce a masanaantar samakon yadda ake ce (kaso mafi yawa) suna goyon bayan Ali da Falalu da masu raayi irin nasu yayin da wani kason da aka ce (mafi kankanta) yake goyon bayan raayi irin da Naziru Sarkin Waka, kuma hakan ne ya janyo tonan asiri daga kowanne bangare ciki harda abin da ya shafi taimako na kudi ko kuma lalata da ake zargin wani daga cikin wani bangare na yakin.

To sai dai wani bincike ya nuna ko dai karancin kudi a Kannywood ko karancin kudi ga masu shirya fina-finan Hausa yasa ake biyan naira dubu biyu ko dubu uku ga jarumi ko kuma ma shi jarumin (musamman mata) ke biyan kudi a saka su a film domin hakan ne zai basu dama a sansu, su kuma suyi amfani da sanin da akayi musu domin yin talla ga kamfanoni ko bude guraren sana’o’i ko kabar kudi daga wajen Yan siyasa ko kuma bada kansu ga masu bukata (AYI LATATA DA SU) domin samun kudin ko kuma wani abu mai kama da hakan.

Bugu da kari da yawa daga cikin su kansu Yan film din sunyi amannar cewa kaso mafi yawa a kudin da Yan film ke samu suna samun sa ne a wajen masanaantar ba cikin ta ba.

Bincike ya tabbatar da cewa kudin da ake kashewa wajen shirya fina-finai a Kannywood bai wuce kudin cin abinci ba a wasu masana’antar wajen shirya film.

Alal misali a shekarar 1997 masana’antar shirya fina-finai ta “Hollywood” karkashin kamfanin “Suny Pictures” ta shirya film mai suna “The Airforce one” wanda aka saki a ranar 25 ga watan yulin 1997, kuma an kashe Dala miliyan 85 Wanda yanzu idan ka canza da kudin Nigeria ya Kai naira Biliyan 3 da miliyan 800 da doriya.

“Airforce one” dai shiri ne Mai nisan awa daya da minti hamsin da bakwai (01h, 57Min).

Haka Kuma film din Titanic da aka shirya a masana’antar Hollywood a shekarar 1997 Wanda James Cameron ya shirya ya rubuta ya kuma bada umarni kuma aka saka a shekarar ranar 1 ga watan Nuwamban 1997 a birnin Tokyo, ya lashe Dala miliyan 200, wanda idan ka canza a kudin Nigeria a yanzu zai baka naira Biliyan tara (9,000,000,000) da mosti zai baka.

To amma wani zaice ai dama baza a hada Hoolywood da Kannywood ba, domin wasu dalilai na sa, to Amma Mai karatu sai ka tambayi kanka bayan Kannywood a Nigeria, ai akwai Noolywood itama masanaanta ce da ke da shalkwata a jihar Legas dake kudancin Nigeria kuma tana shirya fina-finai Kamar Kannywood.

A shekarar 2012 masana’antar Noolywood ta shirya film din “last flight to Abuja” mai nisan mintuna tamanin da daya (81minute) wanda Obi_Emelonye ya shirya ya kuma bada umarni, kuma su obi sun kashe naira miliyan 40 a shirya “last flight to Abuja”.

Kai ba ma wannan ba, a yan kwanakin nan Noolywood sun shirya film sakamakon bullar cutar Korona a disambar shekarar 2020 a birnin Wuhan na kasar China wacce ta mamaye Duniya ciki harda Nigeria lamarin da ya sa aka Sanya dokar kulle ko zaman gida (Lockdown).

Hakan yasa Noolywood shirya film mai suna “Lockdown” Kuma an kashe Dala miliyan uku ($3,000,000) kwatankwacin Naira Biliyan daya da miliyan dari uku da doriya (1,350,000,000).

A nan tambayar da zaka yiwa kanka shine nawa ake kashewa kafin shirya film a kannywood da masu ruwa da tsaki ke inkarin ana bawa jarumai naira dubu (2,000) ko dubu (3,000)?

Amsar hakan na cikin kwarya-kwaryar binciken da nayi wanda ya gano cewa daga ranar farko na fara shirya film a Kannywood zuwa har ranar da zaa saki film din ana kashe kasa da miliyan daya ko naira miliyan daya (1,000,000) ko miliyan biyu (2,000,000) ko sama, harma ana ganin idan aka kashe naira miliyan biyar anyi bajinta Kuma film ne na azo-a-gani.

Alal misali akwai wani shiri Mai suna “Lamba” wanda mallakin Abubakar Bashir Maishadda ne da yanzu haka ana haskashi a gidajen “cinema” da bincike ya gano cewa an kashe wajen naira miliyan biyar (5,000,000). To fa irin wadannan ne ake cewa anyi bajinta kuma anyi abin azo-a-gani.

To yanzu a karamin lissafin Mai lissafi idan ya kwatanta kudin da ake kashe na “Lockdown” naira (1,350,000,000) da na “Lamba” naira (5,000,000) sai ka ce………….

Shawara dai a nan bata wuce ga su masu harkar ba da su manta da bambance-bambancen da yake tsakanin su tare da komawa teburin sulhu gami da saka damba da zata bunkasa harkokin shirya fina-finai, yayin da Gwamnatin jihar Kano da takwarorin ta na Arewa gami da Kamfani ya kamata su duba ta yadda zasu shiga domin samar da dokoki gami da bunkasa harkokin la’akari da dunbum mutanen da ke cin abinci a cikin ta.

Sani Magaji Garko.
sanimgarko@gmail.com.
09023685841.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...