ABUBUWAN DA BA A SANI BA KUMA BA A FADA BA, AKAN YAR FIM BABA TAMBAYA  (LADIN CIMA

Date:

Ali Kakaki.
A yan kwanakin nan, a duniyar yanar gizo-gizo ba’a samu abinda ya tada hazo ba, sama da rikicin daya shigo masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood, tun bayan sakin hirar da Ladi Cima, wanda mutane suka fi sanin ta da Baba Tambaya tayi da kafar yada labarai ta Bbc Hausa a Shafin su na Facebook.
Tun ranar da BBC Hausa, suka saki rahotan nake kokarin har hada hujjoji daga dukka bangare guda biyu, bangaren Ladi Cima da kuma Abokan sana’ar ta.
Abinda na fahimta shi ne, tabbas shaidan ya taka muhimmiyar rawa a bangarorin biyu duba da yadda maganar bata kai ta kawo ba, wacce za’a iya sulhunta ta, a samo mafita cikin abinda bai wuce awa daya ba idan aka zauna aka fahimci juna, mai kuskure a bashi kuskuren sa, sannan a yafi juna a kuma cigaba da mu’amala da juna cikin girmamawa.
A lokacin dana tuntubi Ladi Cima a waya, munyi magana cikin fahimta, kuma cikin alhini take bayyana min cewa yanzu haka ma tana cikin damuwar rashi har guda biyu da suka sameta kasa da wata uku da suka wuce, na farko mahaifin ta Allah ya mishi rasuwa sai kuma babban danta shi ma Allah ya karbi ransa cikin abinda bai wuce kwana goma sha biyar ba da suka wuce, ga kula da yara sama da biyar da suke karkashin ta, ga kuma shekarunta da suka ja.
Tabbas ko iya wadannan abubuwa aka duba, aka dauki daya daga cikin su ya kamata a daraja Ladi Cima a barta hakanan, duk maganar da ta furta a yi mata uzuri akan ta.
Shifa dan halak koyaya yake baya manta halacci, wannan maganar Ladi Cima ta bayyana mun, kuma tana sane da dukkan halaccin da yan film suka yi mata, kuma a kowanne lokaci tana musu fatan Alkhairi kamar yadda ta bayyana min.
A shawarce a ganina, a irin wannan lokaci babu abinda Baba Tambaya take bukata duba da girman shekarun ta irin kwanciyar hankali, kuma idan har bamu zama silar kwantar mata da hankali ba, bai kamata mu zama silar tayar mata dashi ba.
Da yawan matasan yan film dinnan, Ladi Cima ta fara film tun kafin ma a haifi iyayen su, tunda fiye da shekaru hamsin baya ma ana dora mata camera, saboda haka, ko baka girmama ta ba don shekaru ya kamata ka girmamata domin ta shuka alkhairin da a yau shi ne yayi maka riga da wando.
A karshe zanyi tunatarwa da kuma bada Shawarar ga abokan sana’ar Ladi Cima, da farko ku sani cewa babu wata masana’anta kowacce iri ce da zatayi albarka matukar yaran cikin ta basa girmamawa da daraja dattijan cikin ta, ku binciki dukkan wata masana’anta dake duniya, founders dinta sune ginshikan ta wadda tabasu tamkar karya lagon kune, dole a kula da wannan a kiyaye idan ana son ganin dai-dai.
Na biyu a ganina a shawarce mai zai hana mu tausayawa wannan baiwar Allah, ba domin muna raina abunda ake bata ba, a’a sai domin nuna godiya ga irin gudummowar da ta bayar wajen kafuwar wannan masana’anta tun daga jaririyar ta mu taimaka mata da dukkan abunda muke ganin zamu iya bayarwa na tallafi a gareta na abinda ya samu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta dakatar da Dadin kowa, Labarina, Jamilun jidda da wasu fina-finai 19

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   A kokarinta na tabbatar da ana...

2027: Hon Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana Matsayarsa kan takarar gwamnan Kano

Daga Zakariya Adam Jigirya   Dan Majalisar tarayya mai wakiltar kananan...

Sarkin Yaƙin Garko, ya ɗauki nauyin dubawa da raba magunguna kyauta ga marasa lafiyar 1400 a Garko

  Sarkin Yaƙin Garko, mai kishin al'umma, kuma ɗan jam'iyyar...

NAHCON ta yi jigilar Maniyatan Nigeria Sama da 24,000 zuwa Saudiyya a kwanaki 10

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Hukumar Kula da aikin hajji ta...