Daga Fatima Mai fata
An bukaci da a cigaba da taimakawa rayuwar marayu tun kafin su fada cikin wani kangi na rayuwa.
Anyi Kira da al’umma dasu kasance cikin tsarin tallafawa marayu da masu rangwamen karfi duba ga yadda rayuwar su ke kasance a wannan lokaci sabida rashin kulawar da basa samu.
Shugaban gidauniyar tallafawa mabukata daga tushe ( Grassroot Care & Aid Foundation) Amb. Auwal Muhd Danlarabawa ne ya bayyana hakan a lokacin da suke raba kayan sallah ga marayu da masu rangwamen gata guda1500 a wannan wata na Ramadan.
Yace gidauniyar ta dauki shekaru 10 tana gudanar da wannan tallafi na kayan abinci da kayan sallah ga marayun da gidauniyar ke dasu karkashin gidauniyar Wanda ake bawa marayun karatu kyauta a makarantun da gidauniyar ke dasu a kananan hukumomin nassarawa da Ungogo a jihar Kano.
Danlarabawa ya Kara da cewa a wannan wata suna raba abincin ciyarwa na mutane 12000 da kuma raba danyen abinci na mutane 3000 duk a wannan wata na Ramadan
Ambassador Auwal Muhd Danlarabawa ya Kara Kira ga al’umma dasu cigaba da taimakawa rayuwar marayu a kowanne lokaci a kowacce unguwa Dan samun ladan da Allah ya tanadar ga masu tallafawa mabukata.