Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa
Sabon zababben Shugaban Kasuwar wayar hannu ta Farm center Hon. Hassan Ba Wasa ya bada tabbacin zai duk Mai yiwuwa wajen Kawo sauyi Mai ma’ana a Kasuwar tare da tabbatar da walwalar Yan Kasuwar da kwastomominsu.
Kadaura24 ta rawaito Shugaban Kungiyar Kasuwar ya bayyana haka ne Cikin Sakon na Godiya da ya sa Masa Hannu da Kansa ,Kuma aka rabawa Manema labarai a kano.
Yace Nasarar da ya Samu daga Allah ce ba Kuma Dan yafi Kowa Allah ya bashi ba, don haka yasha alwashin tafi da dukkanin ‘ya’yan Kungiyar domin Samar da cigaba a Kasuwar ta Farm center.
” Ina godiya ga dukkanin al’ummar Kasuwar wayar hannu ta Farm center bisa yadda Suka Sha Rana suka Sha tsaiwa domin su Zabe ni da Sauran Shugabannin Wannan Kasuwa Babu shakka Babu abun da Zan ce garesu sai godiya da sa albarka” inji Hassan Ba Wasa
Sabon zabbaben Shugaban yace Zai hada Kai da Sauran abokan takarar sa wajen ganin an samarwa al’ummar Kasuwar kyakykyawan yanayin Kasuwanci, ta hannu Daya kuma zasu yi aiki da dukkanin Masu Ruwa da tsaki a Gwamnati da Kamfanoni don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Game da Sauran al’ummar Jihar Kano da na Kasa Baki daya kuwa Musamman Masu mu’amalar Kasuwanci da kasuwa, Hon. Hassan Ba Wasa yace zai fito da Sabbin tsare-tsare domin tsarkake Kasuwar daga bata gari Waɗanda suke sawa ana zagin Kasuwar da Kuma zargin yan Kasuwar.