Sojoji sun Kama Mutane 10 da ake zargin Yan Boko Haram ne a Kano

Date:

Sojojin Najeriya sun kai wani samame wani masallaci da ke Filin Lazio unguwar Hotoro cikin birnin Kano kuma sun kama kimanin mutane 10 da ake zargin ‘yan Boko Haram ne a yammacin Asabar din data gabata.


 Shaidun gani da ido sun shaidawa Solacebase cewa aikin wanda bai wuce awa daya ba ya gudana yayin da al’ummar musulmin yankibke gudanar da buda baki.


 Lamarin ya haifar da firgici da tsoro ga mazauna yankin, yayin da Sojoji Kuma suka gudanar da bincike a wasu gidaje .


 Solacebase ta rawaito cewa nan da nan bayan aikin, Wasu Daga Cikin al’ummar yankin suka kauracewa unguwar Saboda tunanin sojojin zasu iya komawa unguwar.

 Lokacin da Majiyar Kadaura24 ta tuntube  kakakin rundunar a nanKano Kyaftin Irabor ya yi alkawarin idan ya kammala tattara bayanan Zai sanar da Manema labarai a Ranar Lahadi nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda kamfanin ganyen shayi na Z&Y ke fuskantar matsin lamba daga TOP TEAA

Wani matashin ɗan kasuwa daga jihar Kano, mai suna...

Gwamnatin Kano ta bayyana sunayen unguwannin da aka sami gurbatacciyar Iska

    Wani rahoto na mako-mako kan yanayin lafiyar iska da...

Sallah: Gwamnatin Kano za ta hukunta gidan wasan da ya bar masu shigar banza da shaye-shaye

Daga Rahama Umar Kwaru   A kokarin ta na yaki da...

Sallah: Hussari ya sauke kabakin arziki ga yan jam’iyyar APC na karamar hukumar Gwale

Daga Ibrahim Abubakar Diso   Tsohon Dan Majalisar wakilai da ya...