Kano Correctional tigers ta kara wasan Sada Zumunci da takwararta ta Sharada United

Date:

Nasiba Rabi’u Yusuf
An yi wasan sada zumunci da Kungiyar Kwallon kafa ta hukumar Gidan gyaran hali ta kasa reshen jihar kano wato Kano Correctional tigers da takwararta ta Sharada United.
Kadaura24 t rawaito An dai tashi daga Wasan Canjaras babu wata Kungiya da tayi nasara akan yar’ uwarta.
Wasandai an fafatashi ne
a jiya Alhamis a filin wasa na Sharada United dake Kofar na’isa a birnin Kano.
Bayan kammala wasan a zantawar Kadaura24 da Kaftin din Kungiyar Kwallon kafa ta hukumar Gidan gyaran hali reshen jihar kano AIC Abbas Abubakar Musa ya tabbatar da cewa kungiyarsa ba fa sabuwa bace, domin a baya ita akewa lakabi ada Prison tigers Wanda a yanzu haka ta koma, Kano Correctional tigers a cikin shekarar da ta gabata inda aka farfado da ita.
A dan haka yace Kungiyar a shirye take ta fafata wasa da dukkanin kungiyoyin dake son karawa da ita.
Kuma nan da lokaci kan-kani sai wannan Kungiyar ta bada mamaki a harkar Kwallon kafa a jihar kano da kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...