An Fara bukukuwan cikar Garban Kauye Shekara 1 akan Mulkin K/H kumbotso

Date:

Daga Sayyadi Abubakar
Yan siyasa sun lalllasa ma’aikatan Gwamnati da ci daya mai ban haushi.
A Wani bangare na bikin cikar Shugaban Karamar hukumar Kumbotso Hon Hassan Garban kauye farawa murnar cika shekara guda a matsayin Shugaban Karamar hukuma Kumbotso an shirya wani wasan sada zumunta domin kyautata alakar aiki tsakanin ma’aikatan Gwamnati na Karamar hukumar da Masu mukaman Siyasa.
Wannan dai a kunshe Cikin wata Sanarwa Mai dauke da sa hannun  shugaban kwamitin yada labarai na wasan shazali farawa wadda kuma ya aikowa Kadaura24.
Wasan Wanda ya gudana a filin wasa na Kumbotso, Yan siyasa sun yiwa ma’aikatan Dakan sakwara bayan da aka tashi 1-0, inda Yan siyasa suka samu nasara bayan dawowa daga hutun Rabin lokaci ta hannun kamalu Tanda SA komai da Ruwan ka.
Bayan kammala wasan Shugaban Karamar hukumar Hon Hassan Garban farawa ya Mika Babban Kofi ga matainakinsa a matsayin jagoran Masu mukamai Kuma Captain wato Hon Shamshu Abdullahi Kademi, Yayin da su Kuma ma’aikata suka karbi karami ta Hannun CPO.
Tarihi ya nuna cewa ba’a taba samun wani lokaci da ma’aikatan Gwamnati da yan siyasa suka hadu domin yin wasan Sada Zumunci a karamar Hukumar Kumbotso ba,  sai wannan lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta dakatar da Dadin kowa, Labarina, Jamilun jidda da wasu fina-finai 19

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   A kokarinta na tabbatar da ana...

2027: Hon Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana Matsayarsa kan takarar gwamnan Kano

Daga Zakariya Adam Jigirya   Dan Majalisar tarayya mai wakiltar kananan...

Sarkin Yaƙin Garko, ya ɗauki nauyin dubawa da raba magunguna kyauta ga marasa lafiyar 1400 a Garko

  Sarkin Yaƙin Garko, mai kishin al'umma, kuma ɗan jam'iyyar...

NAHCON ta yi jigilar Maniyatan Nigeria Sama da 24,000 zuwa Saudiyya a kwanaki 10

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Hukumar Kula da aikin hajji ta...