Daga Maryam adamu Mustapha
Uwar gidan Shugaban Kasa Aisha Buhari ta ja hankalin gwamnatin Kano da ta dauki matakan kariya ga Kananan Yara don gudun kara afkuwar abin da ya faru da yarinyar nan Haneefa Abubakar da malaminta ya yiwa kisan gilla a nan Kano.
Uwar gidan shugaban kasa ta bayyana hakan ne lokacin da ta zo Gidan Gwamnatin Jihar Kano don yiwa Gwamnati da Iyayen Hanifa Abubakar ta’aziyyar Rasuwarsu .
Aisha Buhari ta yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa matakan data dauka tun faruwar lamarin, Sannan ta ce saurin yanke hukunci ga Waɗanda aka Samu da Wannan laifi zai kwantar da hankalin iyaye musamman mata.
Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya jaddadawa al’ummar Kano cewa gwamnatin Kano ba za ta kara ko minti guda ba wajen sanya hannu, Idan Kotu ta yanke hukuncin kisa akan Waɗanda ake Zargi.
Uwar gidan Shugaban Kasar ta Ziyarci Fadar Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero domin yi Masa ta’aziyyar rashe-rashen da akai a Kano a yan watannin baya.