Daga Rukayya Abdullahi Maida
Mataimakin Shugaban Kasa farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci Gidan su yarinyar nan Hanifa Abubakar wadda malaminta ya sace Kuma ya kasheta domin yi musu ta’aziyya Rasuwar ta.
Mataimakin Shugaban Kasar ya nuna Rashin Jin dadinsa bisa kisan gillar da aka yiwa Hanifa Abubakar, Inda yace ya kadu sosai da ya Sami labarin kisan da aka yiwa Mata.
Yace Yana da tabbacin Kamar yadda Jami’an tsaro sukai aikinsu na kamo wanda ya aikata Laifin, Suma bangare Shari’a zasu yi nasau Aikin na tabbatar da Hukuncin akan duk Wanda aka Samu da hannu a kisan gillar da aka yiwa Hanifa Abubakar.
Wakiliyarmu ya rawaito nace Farfesa Yemi Osinbajo ya je Gidan su Hanifa ne bisa rakiyar Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.