Daga Sadiya Muhammad Sabo
An kammal Zaman sulhun da ake yiwa bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da na tsagin su Sanata Malam Ibrahim Shekarau, Wanda aka gudanar a yau din nan Juma’a.
Kadaura24 ta rawaito an dai gudanar da zaman sulhun ne karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Yobe Kuma Shugaban Kwamitin Rikon jam’iyyar APC na Kasa Mai Mala Buni, Wanda aka gudanar da zaman a gidan Gwamnatin jihar Yobe dake Abuja.
Zaman na yau dai ya Sami halartar Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Wanda a baya ya tura wakilci domin Fara Zaman sulhun, Inda a wancan lokaci aka saurari korafin kowanne bangare gabanin Wannan Zama na yau.
Rahotannin sun tabbatar da cewa jam’iyyar APC na sun Gudanar da sulhun ne gabanin hukuncin kotun daukaka Kara ya fito domin a samar da dai-daito a jam’iyyar.
Zaman na yau dai bayan Gwamna Ganduje akwai Sanata Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Barau Jibril da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, sai Kuma Shugaban Masu Rinjayen na Majalisar wakilai Hon Alhassan Ado Doguwa da sha’aban Ibrahim Sharada da dai Sauran Masu Ruwa da tsaki a kowanne bangare.
Wasu rahotanni da Kadaura24 ta samu ta karkashin Kasa sun nuna bayan tsahon lokaci da aka bata ana tattaunawar daga karshe dai ba wata matsaya da aka cimma har yanzu.
Wasu dai Suna ganin hukuncin kotun daukaka Kara ne kawai zai iya raba wannna gardamar.