Wasu jami’o’in Kasar Ukraine zasu hada Kai da Jami’ar MAAUN dake Nigeria wajen bincike da inganta harkokin Ilimi

Date:

Daga Khadija Abdullahi
Jami’o’in Ukraine guda biyu, V.N Karazin Kharkiv da Jami’ar Harkokin Kasuwanci da Shari’a ta Lviv, sun bayyana aniyarsu ta hada kai da Jami’ar Maryam Abacha dake kano a Nigeria, ta fannin bincike da sauran harkokin shiga ilimi.
 Wani memba na tawagar Kasar ta Ukraine, Farfesa Valeriy Reznikov na V.N. na Jami’ar Karazin kharkiv ta kasar shi ne ya bayyana hakan a lokacin da suka kai ziyarar aiki jami’ar Maryam Abacha American University dake Jihar Kano.
 Tawagar ta zo Kano ne domin tantance shirye-shiryen jami’ar ta MAAUN na kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da jami’o’insu.
 Ya bayyana cewa rattaba hannu kan yarjejeniyar zai taimaka wajen samar da ilimi mai inganci a duniya ta hanyar amfani da fasahar zamani.
 Farfesa Valeriy ya kara da cewa, haɗin gwiwar da Jami’ar MAAUN zai basu damar yin kwasa-kwasan da suka hadar da Medical Science da security and Sefty, music and entertainment, sai business, culture da Kuma Agriculture da dai sauransu.
Yace idan akai la’akari da Matsalolin tsaro da ake fuskanta a duniya Musamman Nigeria hadin gwiwa tsakanin jami’o’in zai taimaka wajen Magance Matsalolin tsaro da suka addabi kasar nan, Saboda hadin gwiwar zai baiwa MAAUN damar Samar da Cibiyar koyar da dabarun Magance Matsalolin tsaro, Wanda Kuma hakan zai taimakawa gwamnati Kasar nan Musamman ta fuskar bincike tsarawa da hanyoyin Magance Matsalar tsaro.
 A nasa Jawabin, shugaban kuma wanda ya kafa jami’ar ta Maryam Abacha, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya yabawa tawagar jami’o’in na kasar Ukraine da suka zo daga Ukraine zuwa jami’ar ta MAAUN da ke Kano domin duba ingancin jami’ar.
 Farfesa Gwarzo ya yi alkawarin kammala sauran abubun da ya kamata Wanda hakan zai bada damar kulla akala tsakanin jami’o’in biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...