Daga Sayyadi Abubakar Sadeeq
Hukumar kula da Ƙasar Noma ta Kasa Wato (NISS) ta kudirci aniyar wayar da Kan manoma illar da dumamar yanayi yake jawowa wajen samar da wadataccen abinchi a Kasar nan.
KADAURA24 ta rawaito Shugaban tsangayar kimiyyar Kasar noma na jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Nafi’u Abdu ne ya bayyana hakan yayin Wata bitar yini guda da jami’ar ta shiryawa manoman jihohin Kano Kaduna Jigawa da Katsina a nan Kano.
Farfesa Nafi’u Abdu yace dumamar yanayi tana yiwa Kasar noma illa sosai ba kuma a Nigeria Kadai ba har da Sauran kasashin duniya, Inda yace hakan ce tasa Suka Shirya bitar da fadakar da manoman Hanyoyin da zasu bi wajen fuskantar irin waccan Matsalar.
Yace ana sa ran manoman da suka halarci bitar zasu koyar da Sauran manoman da suke jihohin su domin su san daban da zasu kaucewa irin asarar da dumamar yanayi yake haifarwa manoma da Kuma karancin abinchi da yake haifarwa.
” Dumamar yanayi tana baraza ga Samar da wadataccen abinchi ga Ƙasar mu,don haka akwai bukatar mu san dabarun da ya kamata domin Magance Matsalolin da yake haifarwa, Saboda mu kaucewa waccan barazana ta karancin abinchi”. Inji farfesa Nafi’u Abdu
Farfesa Nafi’u Abdu ya Kara da cewa saboda irin Wadancan Matsaloli ya Zama wajibi Hukumar kula da Kimiyya Kasar noma ta Kasa take Shirya irin wadancan bitoci a shiyyoyin Kasar nan Musamman Waɗannan jihohi guda hudu.
Yayin bitar Malamai sun gabatar da makalolin Kan dabarun da manoma zasu yi Amfani da su don kaucewa illar da dumamar yanayi Kan haifar a gonaki, manoma da dama ne dai Suka halacci bitar ta yini guda.
Wasu daga Cikin mahalatta bitar sun bayyana godiyarsu tare da bada tabbacin zasu koyawa Yan uwansu manoma dabarun da Suka koya a wajen bitar domin cimma manufar da tasa aka Shirya bitar.