Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Global Community ta Ziyarci Ofishin Majiya

Date:

Daga Abdulmajid Habib Isa and
Kungiyar kare hakkin Dan Adam ta global community and human rihgt,
dake karkashin jagorancin karibu yahaya lawan kabara takai ziyarar sada zumunci ga sashin rundunar yan sanda masu Kula da Ababan hawa da rayukan Al’umma MTD.
Kadaura24 ta rawaito Shugaban Kungiyar Karibullah Yahya yace sun Ziyarci ofishinne domin kara karfafa Alakar dake tsakaninsu tare da ganin an kara Samar da hanyoyin da za a cigaba da kile cin zarafin Dan Adam ko take masa hakkin Dan adam, Musamman ga Masu ababen hawa.
Comrade karibullah yahaya ya yaba da yadda Ofishin na MTD suke Gudanar da aikinsu kuma ya bada tabbacin zasu cigaba da Sanya Ido Kan yadda Ofishin yake Gudanar da aikinsu.
Da yake mai da jawabi shugaban sashin Jami,an yan sandan na MTD  a nan jihar Kano SP Magaji Musa Majiya yace  yayi matukar farin ciki da ziyarar da kungiyar kare hakkin Dan Adam ta kai Masa.
Ya Kuma bada tabbacin Jami’an Ofishin sa Suna kwatanta bin dokokin Aikin su ,tare da Kare hakkin Dan adam ba tare da gusgunawa Wanda aka Kama da laifin karya dokokin hanya ba.
SP Majiya yace kofarsa a bude take ako wanne lokaci ga dukka mai bukatar ganin an samu nasara dan ganin an cigaba da tsarewa Al’umma rayukan su da dukiyoyinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...