Daga Safiyya Abbas
Shugaba Buhari ya amince da shawarar da Ma’aikatar Sufuri a karkashin Rotimi Amaechi ta bayar na kafa kwamitin bincike da zai binciki yadda ake gudanar da Hukumar Kula da Tashar Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA).
Shugaban kasar a cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Garba Shehu, ya kuma amince da cewa Manajan Darakta, Hadiza Bala Usman ta koma gefe yayin da ake gudanar da bincike, sannan Mohammed Koko zai rike mukamin a Matsayin Mai rukon kwaryar .
Daraktan, Ma’aikatar Kula da zirga-zirgar jiragen Ruwa ne zai jagoranci kwamitin yayin da Mataimakin Daraktan Harkokin Shari’a na ma’aikatar shi zai zama Sakatare.
Sanarwar tace Minista Rotimi Shi Zai sanar da Sauran mambobin kwamitin.