Zaharadeen saleh
A karon farko a kakar wasa ta bana kungiyar kwallon kafa ta kano pillars ta samu maki uku a waje bayan data samu nasarar doke kungiyar kwallon kafa Heartland dake garin Owerri jihar Imo, har gida daci daya babu ko daya a zagayen wasa mako na tara da aka shiga a cigaba da gasar cin kofin kwallon kafa ajin firimiya ta Nigeria, ta kakar wasa ta shekara ta 2021/2022.
Dan wasan kungiyar kano pillars mai suna Mark Daniel daya shigwo wasan a mintina 87 shine ya samu nasarar jefa kwallo daya tilo aragar Heartland, a mintina 90 wanda ya bawa kano pillars nasarar samu maki uku a wasan da suka fafata a asabar din nan.
Yanzu haka bisa nasarar da kano pillars ta samu ta dawo matsayi na shida da maki 13 a gasar firimiya Nigeria.
A sauran wasanin da aka fafata a asabar din nan kungiyar kwallon kafa ta Enyimba International dake garin Aba jihar Abia , ta samu nasarar doke kungiyar Katsina united daci biyu da daya, itama kungiyar Sunshine Stars dake garin Akure jihar Ondo ta lilisa kungiyar Lobi Stars dake garin Makurdi daci uku da nema.
A yammancin ranar Lahadin ce idan Allah yakaimu za’a fafata ragowar wasanin guda bakwai na zagayen wasa mako na tara da aka shiga.