Gyaran Gada: PDP ta zargi Ganduje da almubazzaranci da kudaden Mutanen Kano

Date:

Daga Halima M Sadeeq
 …. Amincewa da N525m don kawata gadar Kofar Ruwa ya wuce gona da iri bata kudi ne.
 Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano na koka da tsananin mamaki, matakin da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya dauka na kashe sama da naira miliyan dari biyar wajen kawata gadar kofar ruwa wadda aka sanyawa sunan Marigayi Galadiman Kano Alh.Tijjani Hashim.
Cikin Wata sanarwa da Shugaban jam’iyyar Alhaji Shehu wada sagagi ya Sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24 yace yana da kyau su jawo hankalin al’ummar Kano cewa kudaden da aka amince da su don kawata gadar ta Kofar Ruwa almubazzaranci ne ga dukiyar al’ummar Jihar Kano.
 Duk da cewa aikin yana da tsada sosai, Amma suna sane da Cewa an fara aiwatar da aikin makonni bayan, kafin daga bisa majalisar Zartarwar ta amince da fidda kudin Wanda baya cikin kasafin shekarar 2021 ko 2022 ba.
 Wannan laifi ne da zai iya dawowa a iya tsige gwamnan, wanda ya kamata a yi taka tsantsan tare da sanya sa ido, ga Majalisar dokokin ‘ majalisar jihar kano.
 “Muna kira ga ’yan kungiyoyin farar hula da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa irin su EFCC da ICPC da su binciki wannan ta’asa ta rashin gaskiya da rikon amana”. Inji Sagagi
 A bayyane yake cewa gwamnan yana kan kashe kashen kudi domin kara durkusar da tattalin arzikin jihar Kano kafin cikar wa’adinsa na biyu don mayar da Kano baya.
 “A matsayinmu na jam’iyyar adawa kuma ’yan jihar Kano nagari, mun yi Allah wadai da wannan aika-aika tare da yin kira ga Majalisar Dokokin Jihar Kano da kungiyoyin farar hula da masu ruwa da tsaki da su yi watsi da wannan aiki domin kuwa Zai kawowa tattalin arzikin Jihar Kano Koma baya.
Idan za ku iya tunawa a makon da ya gabata ne gwamnatin jihar Kano ta amince da kashe makudan kudade har Naira miliyan 525, 435, 750.00 domin kawata gadar Kofar Ruwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...