Rikici ya kunno Kai Cikin Kwankwasiyya, ana Zargin DanGwani da zagon Kasa

Date:

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa

Tafiyar Kwankwasiyya a Kano na fuskantar mummunar rikicin cikin gida tsakanin mambobinta a cikin Yan  makonnin da suka gabata.


 Wannan na zuwa ne bayan daya daga cikin masu ruwa da tsaki da shugabanninta a Kano suka raba kayan abinci na miliyoyin nairori a matsayin wani bangare na tallafin Azumin watan Ramadan ga mambobinta.


 An ga wani na hannun daman Kwankwaso Sanusi Surajo a wani bidiyo da ya yadu a yanar gizo,inda yake zargin Dakta Yunusa Adamu Dangwani da kokarin wargaza tafiyar saboda burinsa na takarar gwamna.


 Sanusi Surajo ya sake jaddada cewa ba za su kara yarda da kowane dan takara ba in ba Abba Kabir Yusuf ba, yana kiran Dangwani ya ajiye da burinsa ko kuma ya fice daga tafiyar ta Kwankwasiyya.


 “Ko Kwankwaso ba zai iya canza mana Abba ba, idan ba za ku goyi bayan Abba ba gara ku fice daga Wannan tafiyar ko ku sauya sheka daga jam’iyyar.


 Abba ya sami goyon bayan mutane, mutane sun yarda da shi, ba za mu iya canza shi ba, amma mun san cewa yana yin wadannan yunkurin ne domin yi wa Kwankwaso zagon kasa amma Allah Yana ganinsu kuma ba za su yi nasara ba.


 Duk da cewa ya ki ambatar suna, amma sakon nasa ya bayyana karara cewa yana bayanine akan Dakta Yunusa Dangwani, tsohon Shugaban Ma’aikatan Kwankwaso kuma Kwamishinan albarkatun ruwa lokacin da kwankwaso yake gwamna a wa’adi na biyu.


 Dangwani ya kasance a a Cikin zargi ne tun lokacin da ya raba kayan azumin Ramadan ga mambobin jam’iyyar.


 Tun daga lokacin ya ji ‘ya’ya da masu ruwa da tsakin Kwankwasiyya suna goyon bayansa dangane da kiransa ya fito takarada takarar gwamnan Kano a Shekara ta 2023


 Tun fitowar sa Matsayin dan takarar kujerar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar PDP, Abba k Yusuf yake ta jin kansa, baya girmama kowa kuma yana amfani da wasu mambobin wajen cin zarafin wasu masu ruwa da tsaki a kokarin da yake na musguna musu.


 Wannan shine dalilin da ya sa bama son Abba, ko da kuwa ya yi nasara, zai ajiye shugabanninmu a gefe, ba Zai yi aiki tare dasu ba.  Wani memban kungiyar da ya Nemi a sakaye sunansa ya fada.


 A cewar wasu, ba Yunusa Adamu Dangwani ne kawai Cikinmai ruwa da tsaki a Kwankwasiyya da basa jituwa da Abba Kabir Yusuf ba,yawancin shugabannin kungiyar suna goyon bayan yunkurin da Dangwanin keyi.


 A wani bangaren Kuma Wasu masu ruwa da tsaki sun nuna rashin amincewarsu da shawarar da Kwankwaso ya yanke na kawo Mohammed Yusuf Jamo a matsayin mataimakin shugaban PDP na shiyyar Arewa maso Yamma da Mustapha Alkassim Dan Hajiya a matsayin Ex-officio.


 A cewar wani na hannun daman Kwankwaso wanda ya nemi a sakaye sunansa yace, Kwankwaso kai tsaye ya kawo mutanen biyu ba tare da tuntubar Masu Ruwa da tsakin a tawagarsa ta Kwankwasiyya ba.


 Wata Majiya ta ce Kwankwaso a shirye yake ya fice daga PDP idan har ya gaza tabbatar da kujerar Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na shiyya ga mutumin nasa.


 Lokacin da Politics DIGEST ta tuntubi daya daga cikin makusantan tsohon gwamnan ko a shirye suke su bi sa tare da ficewa daga jam’iyyar, sai ya ce A’a kuma da yawa daga cikin mutanen sa ba za su bi shi ba idan ya yanke wannan shawarar.
 Daga cikin ‘yan Kwankwasiyya masu adawa da takarar Abba Kabir Yusuf sun hada da Aliyu Sani Madaki, Yusuf Bello Dambatta, Barr.  Maliki Kuliya, Farfesa Umar Farouk Jibril, Danburan Abubakar Nuhu, Zainab Audu Bako, Lawan Sale Gaya, Garba Ibrahim Diso da sauransu.


 Gabanin zaben 2019, makusantan tsohon Sanatan da suka watsar da shi kamar Aminu Dabo, Bala Gwagwarwa, Muaz Magaji da Idris Dambazau sun fice daga tafiyar saboda zabar Abba Kabir Yusuf Matsayin Dantakar gwamnan Kano.

99 COMMENTS

  1. Бій Усик – Джошуа за звання чемпіона світу за версією WBA, WBO та IBF відбудеться в Лондоні. Місцем його проведення стане стадіон футбольного клубу “Тоттенгем”. Щодо дати проведення бою, то JoshuaUsyk Усик та Джошуа провели битву поглядів: відомі деталі

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...