Daga Jamilu Bala
Kotun shari’ar Musulunci da ke Hotoro Masallacin Juma’a ta bayar da umarnin da a kamo mata Jarumin wasan Hausan Sadiq Sani Sadiq.
Wani mai shirya fina-finai Aliyu Muhammad Hannas, ne ya shigar dakarar a gaban kotun kan cewar ya baiwa jarumin kudi domin yayi masa aikin film, amma yaki zuwa don yin aikin, Inda yace hakan ya ja masa asara mai yawa.

Alkalin Kotun Maishari’a Sagiru Adamu, yace Sadiq ya bijirewa Umarnin Kotu duk da sammacin da aka bashi, tare da like masa sammacin a jikinm gidansa amma yaki halartar zaman kotun.
Zuwa yanzu dai kotun ta baiwa Dan sandan Kotun umarnin kamoshi, duk inda yake zuwa gaban kotun.
Express Radio ta rawaito Kotun tace da zarar an kamo Jarumin wasan hausan Sadiq Sani Sadiq, za a cigaba da zaman sauraren shari’ar.
There’s definately a great deal to find out about this
subject. I like all of the points you’ve made.
Its like you learn my thoughts! You appear to understand a lot about
this, such as you wrote the guide in it or something.
I think that you just could do with some p.c. to pressure the
message home a little bit, but instead of that, that is great blog.
An excellent read. I’ll definitely be back.