Daga Surayya Abdullahi Tukuntawa
Shugaban karamar hukumar Kumbotso Hon Hassan Garban Kauye Farawa ya Rantsar da kansiloli 7 Masu gafaka da masu ba shi shawara na musamman, A yau a cikin sakatarorin karamar hukumar, Ya bukace su su yi aiki tukuru domin cigaban Karamar Hukumar.
Da yake jawabi Yayin bikin, Shugaban Karamar Hukumar Hassan Garban Kauye farawa ya yi kira gare su da su zamo Jakadun Kirki ga mutanen Kumbotso.
Wannan yana Kunshi ne cikin wata sanarwa da Hadimin Shugaban Karamar Hukumar a fannin manema labarai Shazali Farawa ya aikowa Kadaura24.
Sabbin wanda aka nada a matsayin kansiloli Masu gafaka sun hada da Surayya Abdullahi P R S, Zainab Saleh kansilar Harkokin Mata, Tukur Aliyu Ilimi, Abdullahi Usman kan Ayyuka da Shu’aibu Bala WESH, Murtala Usaini mai kifi harkokin al’umma da kuma Abba Ibirahim a kan Sashen Noma.
Sauran masu bayar da shawara na musamman da aka amince da su sun hada da Abdussalam Isiyaku Mashawarci na Musamman kan lamuran kasa, al’ummar Abdu Yusuf, Ilimin Rabi’u Aminu, Ibirahim Garba aiyuka. Sauran sun hada da Sani Idiris Mashawarci na Musamman kan Ayyukan Haraji, Zainab Sulaiman Harkokin Mata da Iliyasu Abdullahi. Shugaban Yayi Muku Fatan Alkhairi Wajan sauke Ayyukansu.
Garban Kauye ya lura da cewa, karamar hukumar na bukatar Tallafawa da Gudummawa masu yawa daga gare su a Matsayin su na Masu son ciyar da karamar hukumar gaba.
A halin yanzu Hon Hassan Garban Kauye Na Godiya Ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, Shugaban riko na Jam’iyyar APC na Jihar Kano Hon Abdullahi Abbas Sunusi da Hon Murtala Sule Garo Kwamishinan Ma’aikatar Karamar Hukumar saboda Goyon bayansu da Gudummawar da suka bayar don Ci gaban karamar hukumar Kumbotso karkashin ya adminstration.