Bayan kama Muaz Magaji yan sanda sun bayyana tuhume-tuhumen da suke yi masa

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida
 Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana dalilin da ya sa ‘yan sanda suka cafke tsohon kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa na jihar Kano, Mu’azu Magaji.
 Muaz Magaji, mai sukar Gwamnatin jihar kano, ‘yan sanda sun kama shi ne a Abuja jim kadan bayan kammala hirar kai tsaye da shi a gidan talabijin na Trust da ke Utako Abuja.
 Nan take aka kai shi Kano, kuma ya kwana a hedikwatar rundunar da ke Bompai.
 Da yake zantawa da DAILY NIGERIAN a ranar Juma’a, mai magana da yawun rundunan Jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, ya ce ‘yan sandan sun kama shi ne bayan da tsohon Kwamishinan ya ki mika kan sa ga ‘yan sanda domin amsa tambayoyi lokacin da aka gayyatace shi.
 SP Kiyawa, ya ce ‘yan sandan sun gayyace shi, bisa umarnin kotu na a binciki shi, Amma yaki amsa gayyatar.
 “A yanzu haka muna binciken tuhume-tuhumen da ake yi Masa Waɗanda suka hada da bata suna, cin mutunci da gangan, karya da kuma tayar da kalaman da ka iya tayar d hankali,” in ji kakakin ‘yan sandan.
Idan ba a mantaba Kadaura24 ta rawaito tun a makonni biyu da Suka gabata Muaz Magaji ya wallafa a shafinsa na Facebook Cewa Rundunar Yan Sanda ta Kasa reshen jihar kano ta aike masa da goron gayyata domin ya amsa tambayoyi .

5 COMMENTS

  1. Good post. I learn something new and challenging on websites I stumbleupon everyday.

    It’s always useful to read through articles from other writers and use something from other web sites.

  2. Hey I know this is off topic but I was wondering if you knew of any widgets
    I could add to my blog that automatically tweet my newest twitter updates.
    I’ve been looking for a plug-in like this for quite
    some time and was hoping maybe you would have some experience with something like this.
    Please let me know if you run into anything. I truly
    enjoy reading your blog and I look forward to your new updates.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...