Daga Zara jamil Isa
Kungiyar manoman shinkafa ta Najeriya, RIFAN, ta ce an kammala shirin kaddamar da buhunan shinkafa miliyan daya da aka jibge a matsayin dalar shinkafa wanda ake sa ran shugaban kasa muhd buhari zai a Abuja ranar Talata.
Shehu Muazu, shugaban kwamitin dalar shinkafar, RIFAN ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa dalar shinkafa ya nuna cewa akwai yuwuwar samar da abinci a kasar nan.
A cewar Muazu, bayan kaddamar da dala, babban bankin Najeriya da RIFAN za su ware shinkafar ga masu sarrafa shinkafa yan gida domin gyarata.
RIFAN tare da hadin gwiwar kungiyar masu sarrafa shinkafa ta Najeriya za su sarrafa shinkafar tare da sayar da ita a kan farashi mai rahusa.
“Wannan zai haifar da raguwar farashin shinkafar da zarar ta fara shiga cikin kasuwanni.
“kungiyar da ƙungiyar masu masana’antun shinkafa sun yi yarjejeniyar cewa za mu sayar wa ‘yan Nijeriya shinkafa akan farashi mai rahusa.
“labari mai dadi shi ne shinkafa za ta zamo mafi saukin araha cikin kayayyakin abinchi saboda nasarar da aka samu a tsarin, ”in ji shi.
Mista Muazu ya kuma kara da cewa, shirin Anchor Borrower’s, ABP, wanda aka yi shi domin taimakawa kananan manoma, ya tabbatar da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na magance matsalar karanci da tsadar abinci a Nigeria.