Daga Kabiru Muhammad Get so
Shugaban karamar hukumar Ungwaggo Engr Dr Abdullahi Garba Ramat ya bayyana cewa amfani da sabon tsarin fasahar sadarwar zamani wajen tafiyar da harkokin gudanarwar gwamnati zai taimaka wajen magance matsaloli masu tarin yawa da suke damun al’umma.
Engr. Ramat ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da wakilin Kadaura24, Inda yace tuni shiri yayi nisa wajen tafiyar da shugabancin karamar hukumar akan tsarin fasahar zamani.
Ya Kara da cewar tun a shekaru da dama da suka wuce ya kamata ace tuni shuwagabanni sunyi nisa wajen aiwatar da wannan tsari,domin samun saukin kawar da duk wasu matsalolin da suka addabi al’umma musamman sha’anin matsalar tsaro.
Shugaban ya kara da cewar su yanzu a karamar hukumar Ungoggo tuni sunyi nisa wajen maida duk wasu al’amura a tsarin fasahar zamani,domin hatta takardar shaidar zama cikakken dan karamar hukuma Ana samar da ita ne ta yanar Gizo.
Baya da tarin nasarori da karamar hukumar ta samu a fannin tsaro akwai wata babbar Nasara ta tsarin biyar kudin haraji a kananan injinan musayar hada hadar kudade na Zamani wanda wannan wani tsari ne da zai taimakawa Shuwagabannin dama al’umma baki daya.
Kazalika Shugaban karamar hukumar ta Ungoggo ya ja hankalin Matasa da Su maida hankali wajen Samar da Nagartattun Shuwagabannin a mataki daban daban dake fadin kasarnan. Domim yanzu lokaci yayi da matasa zasu farka su shiga Sahun neman Guraben Shugabanci domin suma a dama da su a sha’anin cigaban kasar nan.
Ya kara da cewar babu shakka yayi imani akwai rawar da matasa zasu taka a lamarin jagorancin kasar nan. Don haka ya zama wajibi su tashi tsaye wajen tabbatar da cancantar fitar da duk wani wakili da zai wakilci al’umma a matakai daban daban dake fadin kasar nan.