Nigeria ce kan gaba wajen yiwa mata auren wuri a duniya

Date:

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta ce auren wuri yana karuwa a Najeriya ne saboda gwamnatin tarayyar da gwamnatocin jihohi ba su dauki wata doka ta hana shi ba.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce Najeriya ce kan gaba a nahiyar Afirka wajen aurar da yara mata da wuri.

Kodayake dokar kare hakkin yara ta 2003 da gwamnatin tarayyar kasar ta yi ta haramta aurar da yara ‘yan kasa da shekara 18.

Su kuwa jihohin kasar da ke amfani da tsarin shari’ar musulunci sun gaza amfani da dokar da gwamnatin tarayya ta yi a kan batu aurar da yara ‘yan kasa da shekara 18.

BBC Hausa ta rawaito Kungiyar ta Human Rights Watch ta ce,” Abin damuwa ne ace kusan shekara 20 da zartar da doka a kasa, amma har yanzu ana aurar da yara mata ‘yan kasa da shekara 18 a kasar”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An sanya dokar hana fita a Jigawa

An sanya dokar hana fita a Jihar Jigawa tare...

Gwamnan Kano ya bayyana abun da gwamnatin za ta yi a filin Idi

  Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanar...

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...