Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Alhaji Hamisu Ibrahim Chidari ya yi kira ga masu sana’ar babura masu kafa uku na adaidaita sahu da su dakatar da yajin aikin da suke yi domin ci gaban jihar.
Alhaji Hamisu Ibrahim Chidari ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
Ya bayyana cewa, majalisar dokokin jihar Kano ta tuntubi hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano (KAROTA), da kuma shugabannin kungiyar masu tuka babur don sasanta rikicin cikin ruwan sanyi.
Ya kara da cewa, za a zauna domin tattaunawa tsakanin bangarorin biyu domin warware rikicin.
Alhaji Hamisu Ibrahim Chidari ya koka kan wahalar da fasinjoji ke fuskanta sakamakon yajin aikin da ya gurgunta al’amura a jihar kano.
Shugaban majalisar ya jaddada kudirin majalisar na ciyar da jihar gaba ta hanyar samar da dokoki da nufin inganta rayuwar jama’a.
Rediyon Najeriya ta rawaito cewa, yajin aikin da masu adaidaita sahu suka shiga a Kano ya jefa fasinjoji cikin mawuyacin hali sakamakon karancin ababen hawa.