Hukumar Zakka ta Rabawa Mabukata 100 Zakka a Kano

Date:

Daga Sayyadi Abubakar

Hukumar Zakka da Hubsi ta jihar kano ta rabawa mabukata 100 zakkar naira dubu goma-goma domin kyautata rayuwarsu da rage musu radadin matsin rayuwa da ake fuskanta a wannan lokaci.

Da yake zantawa da manema labarai Shugaban hukumar Sheikh Yusuf Usman Makwarari yace wani bawan Allah mai suna Alhaji Umar Abba Muhd ne ya kaiwa hukumar zakkarsa ta wannan shekarar.

Ya kuma ce Mutumin ya kawo Zakka a dai-dai lokacin da al’umma suke cikin tsananin bukata saboda matsin rayuwa da ake fama da shi.

Wannan bawan Allah da ya kawo wannan kudin har Naira Miliya daya domin rabawa mabukata,don haka muna kira ga mawadatan dake jihar kano da su rika kawowa hukumar Zakka zakkarsu domin da hakan sai kaga Allah ya yi mana maganin matsalolin da ake ciki”.inji Sheikh Makwarari

A jawabinsa Darakta Janar na hukumar Zakka ta jihar kano Alhaji Safyan Ibrahim Gwagwarwa yace hukumar ta yi tsari na musamman wajen zabo wadanda suka amfana da Zakkar .

Yace an zabo mabukata sosai wadanda aka fahimci suna bukata kuma aka basu zakkar rage musu radadin talauci,inda yace daga cikin wadanda suka amfana har da wani mai fachi da dai masu gudanar da kananan sana’o’i.

“Mun nemo mutane masu tsananin mukata ne saboda su amfana da zakkar, kuma su kara akan jarinsu domin idan Allah yasa musu albarka a abun da aka basu suma wata rana su kawowa hukumar Zakka ta su zakkar”. Inji DG Zakka

Babban Daraktan Wanda shi ne Tafidan Garin Gwagwarwa ya bukaci wadanda suka amfana da Zakka a wannan lokaci da su yi amfani da Zakka yadda ya kamata.

Shi kuwa Mataimakin Shugaban hukumar Zakka Alhaji Mukhtar Abubakar Dan Gwaggo ya bukaci mawadata da suke kano da su daina jinkirtawa ko kara lokacin fitar da Zakkarsu zuwa wata  Ramadhna .

Dan gwaggo yace ita Zakka ana fitar da ita ne idan dukiya ta shekara ,don haka yace ba dalili bane mutane su ki fitar da Zakka sai watan ramadana saboda neman falalar watan na ramadana.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana da zakkar sun godewa hukumar da kuma wadanda ya kai zakkar .

Dama dai aikin hukumar Zakka ne karbar zakkar daga wajen mawadata domin mika ta ga mabukatan dake jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu a Benue

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi...

Rashin Jami’ar Mallakin jihar a shiyyar Kano ta Arewa na kokarin bayar da yankin baya – Alh. Mustapha Ahmad Gwadabe

Daga Shehu Hussaini Ahmad Getso An bukaci Gwamnatin jihar Kano...

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Almuharram a Nigeria

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji...

Yan uwan wata mata sun zargi Asibitin Malam Aminu Kano da sakaci wajen mutuwar yar uwarsu

Daga Sadiya Muhammad Sabo   Yan uwan wata mata da ta...