Daga Maryam Muhd Zawaciki
Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da mahaifiyar Isiyaku Ali Danja, shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin jihar Kano da tsakar daren ranar Talatar data gabata.
Majiyoyi sun ce maharan sun shiga gidan Hajiya Zainab da ke karamar hukumar Gezawa da misalin karfe 1:00 na dare dauke da makamai, inda suka tilasta mata fita daga dakinta suka kuma tafi da ita.
Dan majalisar, Isyaku Ali Danja ya tabbatar da sace mahaifiyar tasa ga ‘yan jarida a ranar Laraba, yana mai cewa har yanzu wadanda suka yi garkuwa da ita ba su tuntubesu ba.
Jaridar Time Express ta rawaito Isiyaku Ali Danja, shi ne tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano kuma wakilin Gezawa a majalisar.