Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta ce ta ƙwato kuɗi da suka zarta naira biliyan 152 daga hannun mazambata a shekarar 2021.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Litinin ta ce baya ga N152, 088,698,751.64 da ta ƙwato, akwai kuma dalar Amurka $386, 220,202.84 da fan na Ingila £1,182,519.75 da Riyal na Saudiyya 1,723,310.
Kazalika, EFCC ta ce ta yi nasarar ƙwace kuɗin intanet na Bitcoin 5,36957319 da kuma Ethereum 0.09012.
Tun farko hukumar ta ce ta yi nasara a shari’o’i 2,220 a faɗin Najeriya a shekarar ta 2021, wadda ita ce nasara mafi girma a tarihinta.