Yajin aikin Yan adaidaita: Nan ba da Jimawa ba Gwamnatin Kano Zata Kaddamar da Sabon Tsarin Sufuri

Date:

Daga Nura Garba Yan Leman
 Nan ba da jimawa ba gwamnatin jihar Kano za ta kaddamar da sabon tsarin sufuri a cikin babban birnin jihar.
 Manajan daraktan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano Karota, Baffa Babba-Dan’agundi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan tsawaita yajin aikin da masu adaidaita sahu suke a kano.
 “Gwamnati za ta kaddamar da sabon tsarin sufurin ne saboda muna son a duba yadda ake tafiyar da harkokin sufuri kamar yadda ake yi a yanzu.
 “Tuni dai shirye-shirye sun nisa wajen samar da ababen hawa.
 “Duk da cewa wasu sun biya kudaden da ya kamata, amma wasu kuma ba sa son biyan kudaden harajin gwamnati, kuma doka ta ce su biya.
 “Yan adaidaita wasun su ba sa son mutunta doka, suna ganin tsaron da suke samu a banza ne kawai”.
 “Ba ni da wani ikon cewa dole su koma aiki haka suma ba su da hurumin fadawa gwamnati abin da zata yi”.inji Baffa
 Babba-Dan’agundi ya ce gwamnati ta damu da tsaro ba wai batun kudaden shiga ba kawai.
 “Wasu daga cikinsu suna aikata laifuka da baburan nasu, shi yasa ba sa son yin rajista,” in ji shi.
 Ya kuma ce Gwamna Abdullahi Ganduje ya umarci hukumar da ta taimaka wa wadanda  aka lalata musu baburansu saboda sun ki yadda su ki shiga yajin aikin.
 Kadaura24 ta ruwaito cewa an samu raguwar cunkoson ababen hawa a garin kano sakamakon yawaitar babura masu uku a jihar.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kwamitin PTA na Kano ya dauki matakan hana ragewa dalibai hanya bayan taso su daga makaranta

DAGA ABDULHAMID ISAH Shugaban Kwamitin Iyayen yara da Malamai na...

Fada daba: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf – Daga Zainab Nasir Ahmad

Daga Zainab Nasir Ahmad Mai Girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Abba...

RATTAWU ta Kano ta taya Abbas Ibrahim Murnar sabon mukamin da NUJ ta ba shi

Kungiyar ma'aikatan Radio da Talabijin ta kasa reshen jihar...

NUJ ta kasa ta baiwa Abbas Ibrahim sabon mukami

Daga Aliyu Abdullahi Danbala   Kungiyar yan Jarida ta Nigeria ta...