Yajin Aikin Yan adaidaita: Yan Sanda Sun Kama Mutane 40 a Kano

Date:

Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Kano ta ce ta kama kimanin mutum 40 bisa zargin afka wa wasu masu sana’ar babur mai kafa uku, saboda kin shiga yajin aikin da suke yi, tare da yi wa masu tafiya a kafa kwace.

Jami’in hulda da jama’a na Rundunar  SP Abdullahi Haruna kiyawa ne ya bayyana hakan kamar yadda BBC Hausa ta rawaito a litinin din nan.

Tun dai da safiyar yau Litinin aka girke jami’an tsaro na ‘yan sanda da na rundunar tsaro ta civil Defense a wasu daga cikin manyan titunan Kano, don jiran ko ta kwana na yiwuwar samun rikici a lokacin da masu babur mai kafa uku a jihar kano suka fara yajin aiki.

A cewar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kano, mutanen da suka kama suna dauke da makamai inda suke tare hanya suna yi wa mutane kwace da tilasta wa masu kananan motoci daukar kaya sauke mutanen da suka dauko don rage musu hanya.

Kadaura24 ta rawaito dama al’ummar jihar kano sun yi hasashen samun irin wannan matsala ta kwacen waya ,wadda dama an dade ana kokawa da ita duk kuwa da kokarin da jami’an tsaro ke yi don magance matsalar.

1 COMMENT

  1. Allah sarki malam talaka ko yaushi Kai ne a wahala Dan sanda Dan karoto da sauran Jami,an tsaro babu Wanda ake takurawa Sai malam shehu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...