2023: Mai Nada Sarki  Zai Iya Zama Sarki – inji Tinubu

Date:

Daga Asiya Takalmawa
 Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, ya yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi a wasu bangarori na cewa ya kamata ya ci gaba da zama jagora a maimakon ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2023.
 Bola Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labaran fadar shugaban kasa bayan wata ganawar sirri da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa ta Villa Abuja ranar Litinin din nan.
 A cewar jigon na jam’iyyar APC, shi dan Najeriya ne kuma yana da ‘yancin tsayawa takara da kansa, ba wai kawai ya tsaya matsayin jagora ba.
 “A ko’ina a duniya Ban taɓa ganin dokar da ta ce wai jagora ba zai tsaya takara ba sai dai ya tsaya a matsayin jagora, ba a haka don haka zan cigaba da neman Shugaban kasa kamar yadda na fadawa shugaba buhari ”. Inji Tinubu
 Jigon na jam’iyyar APC ya ce ya je fadar shugaban kasa ne domin sanar da shugaban kasa a hukumance bukatarsa ​​ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
 Da aka tambaye shi ko shugaban kasar ya aminta da bukatar tasa,  Tinubu ya ce shugaban kasar bai  nemi ya ajiye bukatar tasa ba ta tsayawa takara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Mun Gamsu da Samar da Kungiyar Kwarya ta bi Kwarya – Mai Rago

Daga Zaharadden Sale   Samar da kungiyoyin mata, abune da zai...

Yadda Mijina ya sake ni bayan ya damfare ni – Mansura Isa

Fitacciyar jaruma a Masana'antar Kannywood, Masurah Isah ta tabbatar...

Rashin wadataccen Abinchi ne ke haifar matsalolin tsaro da tattalin arzikin a Nigeria – Shugaban ACreasal

Daga Kamal Umar   Babban jami’in Shirin bankin duniya mai kula...

Kungiyar kafafen yada labaran yanar gizo ta bukaci gwamnatin Kano ta gyara hanyoyin dake karkara

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kungiyar kafafen yada labarai na yanar...