Daga Zainab Muhd Darmanawa
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso, ya ce ba ya nadamar goyon bayan Gwamna Abdullahi Ganduje har ya zama Gwamnan jihar kano.
A lokacin da Sanata Kwankwaso yake tattaunawa da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi, ya yi jawabi game da dangantakarsa da Gwamna Ganduje a baya, da kuma yadda suka yi aiki tare har zuwa 2015.
“Ba ni da wani nadama ko kadan saboda har yanzu muna da karfi, mun fi 2015 karfi. Ba wai a Kano kadai ba har ma a fadin kasar nan da ma wajen,” in ji shi.
An fara zaben Kwankwaso a matsayin gwamnan jihar kano a shekarar 1999 kuma an sake zabersu a shekarar 2011, inda ya cika shekaru takwas da yana mulkin jihar kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba shi dama.
Lokacin da Ganduje ya zama gwamna, Kwankwaso a lokacin Sanata ne mai wakiltar Kano ta tsakiya a shekarar 2015.
Duk da cewa an zabe shi a jam’iyyar PDP, mataimakinsa na lokacin, Abdullahi Ganduje, ya gaje shi a 2015 a matsayin dan takarar jam’iyyar APC.