Yanzu-Yanzu: Abdullahi Abbas ya Zama Shugaban Kungiyar Shugabannin Jam’iyyun dake Kano

Date:

Daga Sani Magaji Garko

 

Majalisar gamayyar jami’iyun siyasa ta kasa ta zabi Abdullahi Abbas a matsayin shugaban majalisar reshen jihar Kano.

Kadaura24 ta rawaito da yake rantsar da sabbin shugabannin wakilin majalisar na kasa wanda kuma ya jagoranci gabatar da zaben Nasar Sidi Ali ya ce dukkan shugabannin an zabe su ne bayan cika dukkan ka’idojin majalisar.

Nasar Sidi Ali ya ce dan takarar jam’iyar APC Abdullahi abas shine yayi nasara da kuri’u 13 daga cikin kuri’u 14 da aka kada a zaben.

Da yake tattaunawa da manema labari bayan an rantsar da shi, Abdullahi Abbas ya ce gamayyar jam’iyun karkashin jagorancinsa zaiyi duk mai yuwuwa domin cigaban dimokuradaiyya.

Abdullahi Abbas ya ce duk da cewa kowannen su yana da jam’iyar sa amma hakan bazai hana su cigaban da aiki tare ba domin cigaban majalisar da ma jihar Kano baki day aba.

An dai zabi Abdullahi abbas na jam’iyar APC matsayin shugaba sai Isa Nuhu Isa a matsayin matemakin shugaba da sai nuhu idris adam na jam’iyar APM a matsayin sakatare da Abdullahi A sharif na jam’iyar AAC a matsayin matemakin sakatare.

Sauran shugabannin sun hada da Ao Muhammad na jami’iyar NRM a matsayin ma’ajiyi da Bello Ado Usaini na jami’iyar a matsayin sakataren shirye-shirye sai sakaten kudi wanda aka zabi Nasiru Aliko na jami’iyar ADP da Ibrahim Muhammad na jami’iyar APP da aka zaba a matsayin sakataren yada labarai na majalisar da kuma Salisu Umar na jami’iyar YPP matsayin mai bada shawara a harkokin shara’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu a jihar

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da...

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...