An Samu Raguwar Karya Dokokin Hanya a Makon da ya Wuce a Kano – Karota

Date:

Daga Rabi’u Sani Hassan
Hukumar dake lura da titunan jihar kano wato karota, tace an sami raguwar karya dokoki hanya da kaso 35 cikin 100 a cikin wannan mako.
Jaki’in hulda da Jama’a na hukumar Nabulusi Abubakar Kofar Na’isa ne ya bayyana hakan yayin da yake bayani kan nasarorin da hukumar samu tun daga farkon wannan makon da muke bankwana da shi.
“ A farkon wanna mako da muke bankwana dashi hukumar karota ta sami nasarori daban-daban a yayin da take gudanar da ayyukan ta”.
Nabulusi yace babbar nasarar da suka Samj ita ce samun raguwar masu aikata laifin da ake kamawa akan hanyoyin jihar kano a wannan mako, Inda yace ya kara raguwa da kaso 35 cikin 100.
Idan ka kwatanta da yawan mutanen da hukumar ta sami nasarar kamawa a makon daya gabata zaka ga sun fi wanda hukumar ta kama a wannan mako da muke bankwana dashi yawan don haka Wannan Babbar nasara ce a gare mu”. Inji Nabulusi
Jami’in hulda da Jama’ar na karota ya Kara da cewa tun farkon wannan mako hukumar bata sami rahaton wata rashin jitawa tsakanin matuka ababan hawa da jami’an ta ba ko kuma al’ummar jihar kano.
Daga bisani na nabilusi Abubakar K/naisa ya bayyana wannan nasara nada alaka da yadda hukumar ta dukufa wajen ganin ta inganta ayyukanta ta fauskar horas da jami’an ta dabarun aiki a duk mako.
Kadaura24 ta rawaito Idan za’a iya tunawa tun a shekarar 2012 da gwamantin jihar kano ta samar da dokar hukumar ta Karota a, hukumar ta dukufa wajen ganin ta samar da ingantaccen yanayin zirga-zirgar ababan hawa a titunan jihar kano.
Sai dai al’ummar jihar na kallon hukumar matsayin kadangaren bakin tulu, ta yadda jami’an ta ke tsawwala musu a fannin kasuwanci da kuma al’amuran su na yau da kullum, duk dai da hukumar ta sha musanta lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...