Hadirin Mota a Kano yayi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 19, Mutane 26 Kuma Suka Sami Raunuka

Date:

 

Haɗarin mota ya yi sanadiyar rasuwar mutum 19, inda 26 kuma su ka ji raunuka a wani haɗarin mota a Bagauda, kusa da Makarantar Horas da Lauyoyi a kan titin Kano-Zariya.

Babban Kwamandan Hukumar kare Haɗarurruka, FRSC, a Jihar Kano, Zubairu Mato ne ya baiyana hakan a wata sanarwa da a ka raba wa manema labarai a yau Alhamis.

Ya ce motoci biyu haɗarin ya rutsa da su, waɗanda su ke ɗauke da lambobi kamar haka, KBT 152 XA da kuma NSR 275 ZX.

Mato ya ce rundunar ta samu kiran gaggawa ne da misalin 7:30 na a yau 6 ga watan Janairu, inda ya ƙara da cewa “Mu na samun rahoton, sai mu ka yi maza-maza mu ka tura jami’an mu da motoci, inda mu ka isa wajen haɗarin da misalin ƙarfe 7: 40 ma safe domin ceton fasinjojin.”

Ya yi bayanin cewa haɗarin ya afku ne sakamakon gudun wuce-sa’a da kuma ganganci, abinda ya haifar da karo goshi da goshi, inda duka motoci biyun su ka kama da wuta.

Ya ce mutane 45 ne a cikin motoci biyun, daga cikin su, 14 maza magidanta, mata magidanta 4 sai kuma karamin yaro namiji duk sun rasa rayukansu, inda 26 kuma su ka ji raunuka.

Ya ƙara da cewa wadanda su ka ji raunuka ai kai su asibitin Kura a na kulawa da su, yayin da gawawwakin waɗanda su ka rasu, an mika su ga iyalan su a caji-ofis na Bebeji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...