Daga Rukayya Abdullahi Maida
Kungiyar Dattawan Arewa (N.E.F) a ranar Laraba ta yiwa gwamnatin jihar Kano ta’aziyyar rasuwar wasu jiga-jigan ‘ya’yanta Yan Jihar Kano da suka Koma ga mahalicci.
A yayin da yake jagorantar tawagar, Shugaban Kungiyar, Farfesa Ango Abdullahi wanda Wazirin Bauchi ya Alh.Muhammad Bello Kirfi ya Wakilta, ya ce sun je gidan gwamnatin Kano ne domin mika ta’aziyyar rasuwar wasu dattijan jihar da suka rasu kwanan nan.
“Mun zo nan ne domin ta’aziyyar rasuwar Sarkin Bai, Alh.Muktar Adnan wanda mutum ne mai daraja, da Kuma babban likita wanda aka assasa Wannan Kungiyar da shi, Dr.Ibrahim Datti Ahmad da kuma cikakken dan siyasa, Alh.Bashir Othman Tofa.”
“Sarkin Bai uba ne a gare mu,Dr.Ibrahim Datti Ahmad ya kasance mai himma a dukkan ayyukanmu yayin da Alh.Bashir Tofa ya kasance Mai hangen nesa da kishin Kasa da son cigaban al’umma”.inji Ango Abdullahi
“Wadannan jiga-jigan mutane sun taimaka matuka gaya wajen ci gaban Arewacin Najeriya da ma kasa baki daya.
Ya kara da cewa suna alhinin rasuwar wadannan manyan mutane wadanda suka bada gudumawa tare da yin tasiri ga ci gaban bil’adama a Kasar nan baki daya.
“Za mu ci gaba da addu’ar Allah Ta’ala Ya gafarta musu ya karbi ayyukansu na alheri ya kuma ba su Jannatul Firdaus ya kuma baiwa jihar da iyalansu hakuri jure Rashin su .”Inji Ango Abdullahi
Farfesa Ango ya kuma yabawa gwamnatin jihar Kano bisa wannan tarba da aka yi musu.
Cikin wata sanarwa da Babban Sakataren yada labaran Mataimakin Gwamna Hassan Musa fagge ya aikowa Kadaura24 yace da yake mayar da Jawabi, gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana jin dadinsa bisa ga Ziyarar ta’aziyya da Kungiyar Dattawan Arewa ta Kawo wa gwamnati da al’ummar Jihar Kano.
“Hakika mun rasa wasu dattijai wadanda basu da son kansu sun bayar da gudunmawa sosai wajen cigaban jihar Kano da Kasa baki daya”. Inji Dr Gawuna
Muna kuma yi musu addu’ar samun rahamar Ubangiji na har abada inji shi.