Daga Umar Hussain Mai Hula
Gabanin zaben shugaban kasa na 2023, ana ta yada jita-jitar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yana zawarcin tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan a sirrance don ya dawo zuwa jam’iyyar APC.
Sai dai kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC, ta gargadi tsohon shugaban kasa Jonathan da kada ya bari a shawo kansa ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC da nufin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
Sun tabbatar da cewa wannan matakin zai yi tasiri sosai wajen rage masa kima a matsayinsa na dattijo
Darakta Janar na PDF, Salihu Lukman wanda ya bayyana hakan a kan koma bayan da ake ta rade-radin cewa Jonathan Zai koma APC, ya ce kada jam’iyyar ta bar tsohon shugaban kasar ya rage Mata kima ta hanyar tsayar da shi takara a kowane zabe a Najeriya.
Sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su rika tattauna Kan abun da zai taimake ya taimaki shugabanninsu.
Idan dai za a iya tunawa, Jonathan ya amince da shan kaye tun kafin a bayyana sakamakon zaben shugaban kasa na 2015 a hukumance ba; Wanda hakan yasa ya samu karbuwa a kasa da ma duniya baki daya.
Bayan wasu ‘yan watanni ana ta cece kuce a tsakanin su, musamman kan yadda aka Zargi PDP ta karkatar da kuɗin al’umma a lokacin da take mulki, Buhari ya rika nunawa kamar sun yi sulhu da Jonathan.
Jagororin biyu sun kasance suna ganawar Sirri akai-akai a fadar Aso Rock Villa.
Duk da dai har yanzu Jonathan bai yi magana kan rade-radin da ake yi masa na yin na komawa da jam’iyyar APC ba, amma shugabannin Kudancin kasar sun bi sahunsa wajen ba shi shawarar Kar ya sake ya dauki wannan matakin
Its like you read my mind! You seem to know so much about this,
like you wrote the book in it or something. I think that you can do with a few pics to drive the
message home a little bit, but instead of that, this is great blog.
A great read. I will certainly be back.