Covid-19: An Daina Hada Sahun Sallah a Masallacin Ka’aba da na Annabi dake Madina

Date:

An dawo da dokar tilasta bayar da tazara da saka takunkumi a Masallacin Ka’aba a Makkah da kuma na Annabi a Madina, kamar yadda hukumomin da ke kula da Masallatan Biyu Masu Daraja na Saudiyya suka bayyana.

Matakin zai fara aiki ne daga ranar Alhamis, inda hukumomin suka ce yanzu saka takunkumi da bayar da tazara ya zama wajibi.

Hukumomin sun ce matakin ya shafi masu aikin Umrah da masu ɗawafi da sauran masu Ibada a masallatan biyu.

Sannan an yi gargaɗi ga baƙi da ma’aikatan Masallatan biyu su mutunta dokar.

Dokokin za su rika aiki a cikin gidaje da kuma waje inda mutane ke mu’amalar yau da kullum.

A ‘yan kwanakin nan masu kamuwa da korona na karuwa a Saudiyya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...