Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani direban tankar mai, mai suna Dahiru Aliyu dan shekara 45 a Hotoro NNPC.
Tabbatar da hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar a ranar Talata.
“Lamarin ya faru ne da safiyar Litinin.
“Mun samu kiran gaggawa daga wani Shu’aibu Muhammad da misalin karfe 10.59 na safe, kuma mun aika da tawagar mu zuwa wurin da lamarin ya faru nan take,” inji shi.
Dailynews24 ta rawaito Abdullahi ya kara da cewa Aliyu ya shiga daya daga cikin dakuna dauke da kwantena da kumfa don goge man da ya zube a lokacin da ya shake ya mutu.