Daga Rabi’u Usman
Anyi Kira ga yan Kasuwa Musamman Kasuwar Kantin Kwari dasu Kasance Masu yiwa Jama’a Sauki Dai-dai Lokacin da ake Cikin Hada Hadar Siyayyar Kayan Sallah a Wannan lokaci na Karatowar Bikin Sallah Karama.
Shugaban Hadaddiyar Kungiyar ‘yan Kasuwar Kantin Kwari Alhaji Sharu Kabiru ne yayi Kiran a ta Bakin Mai Magana da yawun Kungiyar Mansur Dan Dago Jim Kadan Bayan Fitowar Su Daga Gidan Mai Martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero da Mai Martaba Sarkin Bichi Alh Nasiru Ado Bayero yayin Ta’aziyyar Mahaifıyar Su Hajiya Maryam Mai Babban Daki.
Yana Mai Cewar, a Shekarar da ta Gabata Basu Samu Damar Gudanar da Kasuwancin Su ba Sakamakon Annobar Cutar Corona Virus data Addabi Duniya Baki Daya Sai a Wannan lokaci, yace ta Haka ne Zasu Saukakawa Jama’a Musamman a Wannan Lokacin da ake Cikin Watan Azumin Ramadana Mai Albarka.
Ya Kara da cewa, Sunyi Kira ga Kafatanin Masu Kamfanoni dasu Kasance Masu Saukakawa Jama’a Musamman yan Kasuwannin da Suke Siyayyar Kaya a Wajen Su (Diloli) a Sassan Jihohin Kasar Nan.
A Karshe dai Dan Dago yayi Kira ga Al’umma dasu Gujewa Fadawa Hurumin da ba Nasu ba, Musamman Masu Dogon Hannu a Kasuwanni da Suji tsoron Allah Su daina.