Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa rundunar sojin Najeriya bisa gaggawar da ta yi wajen dakile hare-haren ’yan bindiga da aka samu a wasu sassan jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi babban kwamandan Runduna ta 1, Manjo Janar Abubakar Sadiq Muhammad Wase a gidan gwamnati.
Janar Wase, wanda ya ce ya je Shanono da Tsanyawa, domin duba yanayin tsaro a yankin, ya fadawa gwamnan cewa ya tuna da lokacin da mahaifinsa marigayi Kanar Muhammad Abdullahi Wase ya jagoranci jihar a 1994.
Ya ba da tabbacin zai yi aiki tukuru domin gance duk wata barazanar tsaro dake tasowa a wasu sassa na jihar Kano.
China ta mayar wa Amurka martani kan barazanar hari da ta yi wa Nijeriya
Da yake jawabin Gwamna Yusuf ya gode wa jami’an tsaro bisa jajircewarsu, tare da mika godiya ga Shugaba Bola Tinubu bisa nadin manyan hafsoshin tsaro da ya ce suna aiki tukuru.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta ba da motoci Hilux 10 da babura 60 ga rundunar hadin gwiwa da ke aiki a yankunan da abin ya shafa, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro wajen yaki da ’yan bindiga, garkuwa da mutane da kuma satar shanu.