Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya ta musanta zargin da Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi cewa jami’anta sun hana ta tafiya tare da karɓe mata fasfo dinta a filin jirgi.
Mai magana da yawun hukumar, Akinsola Akinlabi, ne ya bayyana hakan ga gidan Talabijin na Channels a ranar Talata .
Ya bayyana cewa abin da ya faru kawai tsarin binciken shige da fice ne da ake gudanarwa ga kowane fasinja.

A cewar Akinlabi, “Hukumarsu ba ta karɓe fasfo din sanata Natasha ba. bincike nna shige da ficen da ake yi ga kowa, sannan aka amince ma ta ta yi tafiyarta.”
Ya ƙara da cewa jami’an hukumar suna yin aikinsu ne bisa ka’ida, kuma yuwuwar karbar fasfo na ɗan lokaci domin tantancewa ba yana nufin an kwace shi gaba daya.
China ta mayar wa Amurka martani kan barazanar hari da ta yi wa Nijeriya
“Jami’anmu dole ne su aiwatar da binciken su. Suna iya karbar fasfo domin duba bayanai, amma hakan ba yana nufin kwacewa ba. Bayan an kammala bincike an bar ta ta tafi,” in ji shi.
Hukumar ta kuma ce sanatar ta yi bidiyon korafinta ne a lokacin da ake gudanar da binciken, kuma tuni an bar ta ta wuce domin tafiya inda ta ke so.
Da aka tambaye shi ko sanatar ta ƙi mika fasfon nata domin duba shi, mai magana da yawun ya ce ba shi da tabbacin hakan.
“Ban san wannan ba. Amma jami’anmu suna da hurumin karɓar fasfo domin tantancewa, sannan su mayar bayan sun gama kuma haka suka yi,” in ji shi.