Saminu Ibrahim magashi
Gamayyar kungiyar tsofaffin sojojin dake fadin kasar nan sun gudanar da zanga zangar lumana, Sakamakon rashin biyansu wasu hakkoki da suka ce Gwamnatin tarayan ta gaza .
Zanga-zangar da Gamayyar ta hadar da Kungiyar tsofafin Sojojin Sama, da Sojojin Ruwa, da kuma Sojojin Kasa. suka gudanar .
Masu zanga-zangar sun zagaya wasu muhimman gurare da suka hadar da Gidan gwamnati da Gidan sarki. Harma ya yin zuwansu gidan sarkin suka sami Wakilin Sarki Alhaji Mahe Bashir Wali ya tarbe shu a madadin Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayaro.
A jawabin Kodinetan Kungiyar a matakin jiha, Junaidu Umar ya bayyana cewa sun fito wannan zanga zanga ta Limana Sakamakon gazawar da Gwamnatin Tarayya ta yi na Kasa biyan su hakkokin su yasa suka fito don nuna damuwar su ga Mahukunta.
“Mun hidimtawa Ƙasar nan tun Muna da karfin mu tsahon shekaru 35 Amma har Yanzu hakkokin mu sun makale ,Kuma hakan yasa da yawa daga cikinmu shiga halin kakanikayi “ini Junaidu Umar
A karshe tsofafin sojojin na fatan Gwamnatin da tarayya da sauran masu ruwa da tsaki dasu tallafa danganin ancire musu hakkokin nasu.
כחלק מהשירות, אנו מעניקים משלוחים בכל הארץ עד לבית הלקוח ושומרים עבורך על דיסקרטיות מלאה. דירות דיסקרטיות במרכז