Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu da maza bakwai da ake zargi da aikata ayyukan badala a wani samame da aka kai wani gida da ke Hotoro Walawai, dake Karamar Hukumar Nassarawa.
An gudanar da samamen ne bayan korafe-korafen da mazauna yankin suka kai kan cewa ana yawan gudanar da ayyukan badala a gidan. Bayan bincike, an gano cewa gidan na wani gwauro ne wanda aka ba shi haya ta hannun dillalin gida.
Lokacin da aka tsare su, wadanda ake zargin sun amsa laifin, suna neman afuwa tare da cewa shaidan ne ya rude su. Sun yi alkawarin ba za su sake aikata irin wannan ba idan an yafe mu su. Sun bayyana cewa kowane zama yana biyan kuɗi Naira 3,000 — inda Naira 1,000 ke zuwa hannun “Magajiya” (matar da ke kula da wurin) a matsayin kuɗin ɗaki.
Abin takaici, a cewar jami’an Hisbah, shi ne bambancin shekaru tsakanin wadanda aka kama — mafi yawan samarin na ƙasa da shekaru ashirin da biyar, ɗaya daga cikinsu ma yana da shekaru goma Sha takwas, yayin da dukan matan da aka kama suke da shekaru sama da 40, kuma sun fito daga jihohin Borno da Adamawa.
Hukumar Hisbah ta jaddada aniyarta ta ci gaba da yaki da ayyukan rashin ta ido da ayyukan badala a cikin Jihar Kano. Haka kuma hukumar ta shawarci iyaye da su rika lura sosai da halayyar ’ya’yansu da abokan da suke mu’amala da su.
Hukumar ta kuma yi kira ga masu gida da su rika bincike sosai kafin su ba wani haya, sannan su rika lura da masu zama a gidajensu don gujewa aikata ayyukan da suka sabawa addini da al’ada.
A ƙarshe, hukumar ta roki jama’a da su rika kai rahoton duk wani al’amari da ya saba wa addini ko al’ada, don tabbatar da tsaftar al’umma.