Gidan Radiyo Guarantee Radio dake Kano ya sanar da nadin Abubakar Balarabe Kofar Naisa a matsayin Babban Manajan tashar, wanda zai fara aiki daga ranar 8 ga Oktoba, 2025.
Abubakar Balarabe Kofar Naisa kwararren dan jarida ne da dade yana ba da gudunmawa a fannin yada labarai, shugabancin kafafen watsa labarai.
Nadinsa ya nuna kokarin tashar na ƙarfafa jagorancinta da kuma ci gaba da jajircewar ta wajen samar da shirye-shiryen da ke ilmantarwa, nishadantarwa da kuma faɗakar da al’umma a fadin Jihar Kano.
Yayin da ya karɓi aiki a yau, Kofar Naisa ya nuna godiya bisa amincewar da aka yi da shi har aka ba sashi jagorancin tashar, sannan ya yi alkawarin yin aiki tukuru tare da sauran ma’aikata da shugabannin tashar don ci gaba da tabbatar da hangen nesa na guarantee radio wajen aiki da ƙwarewa don hidimtawa al’umma.
Ya ce a karkashin jagorancinsa Guarantee Radio 94.7 FM zai ta tabbatar da ta ci gaba da bin ƙa’idodin aikin jarida don cigaban al’umma masu sauraron tashar.