Dubban mutane daga sassa daban-daban na Nigeria sun halarci taron addu’ar uku na marigayi Sarkin Gabas na masarautar Kano, Hakimin Kabo, Alhaji Idris Adamu Dankabo, da aka gudanar a ranar Lahadi a Kano.
An gudanar da taron ne a gidajen marigayi mahaifinsa, Alhaji Muhammadu Adamu Dankabo, inda Malam Umar Ali tare da wasu manyan malamai suka jagoranci addu’o’i da karatun Alkur’ani domin roƙon rahamar Allah ga marigayin, mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa.
Manyan baki da suka kai Jiya ta’aziyyar marigayin ga yan uwansa sun haɗar da tsohon Ministan Shari’a na Nigeria, Mohammed Bello Adoke, Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf da Mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, sai mai taimakawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai, Abdul’Aziz Abdul’Aziz, da kuma tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Haka zalika, fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Dangote, da tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Rt. Hon. Kabiru Alasan Rurum, duk sun ziyarci yan uwan Marigayin domin Mika ta’aziyyarsu.
Marigayi Idris, mai shekaru 48, ya rasu ne sakamakon haɗarin mota da ya rutsa da shi a daren ranar Alhamis a cikin birnin Kano. An yi jana’izarsa a Fadar Sarkin Kano, dake Kofar Kudu, ranar Juma’a, inda Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sunusi II, ya jagoranci sallar tare da taron dubban jama’a.
Iftila’i: Kifewar Kwale-Kwale Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Yan Mata 11 a Kano
Marigayi Idris shi ne ɗa na fari ga tsohon shugaban kamfanin jiragen sama na Kabo Air, kuma Jarman Kano, marigayi Alhaji Muhammadu Adamu Dankabo, wanda ya shahara a harkokin kasuwanci, Sarauta da taimakon al’umma ba a jihar Kano kadai ba har ma da Nijeriya baki ɗaya.
Kamfanin Kabo Air wanda aka kafa a shekarar 1980 ya kasance ɗaya daga cikin manyan kamfanoni jiragen sama a Nijeriya, inda ya yi zirga-zirgar cikin gida, da yankin Afrika da kuma kasashen turai kafin daga bisani ya maida hankali kan jigilar alhazai da kwangila a farkon shekara ta 2000.

Har ila yau, tarihin ya nuna cewa Kabo Air shi ne kamfanin farko da ya mallaki manyan jiragen Boeing 747 guda biyar, abin da ya sanya marigayi Alhaji Dankabo zama ɗaya daga cikin fitattun wadanda suka mallaki jiragen sama masu dogon zango a Nahiyar Afrika.
Sarautane Sarkin Gabas da marigayi Idris ya riƙe na ɗaya daga cikin muƙaman sarautu a tsarin masarautar Kano, wanda ke ɗauke da alhakin Kula da al’adu da gudanarwa. Mutuwarsa a irin wannan ƙuruciya ta bar gibi a cikin tsarin jagoranci na sarautar gargajiya a masarautar Kano wacce har yanzu na ɗaya daga cikin masu masarauti masu tasiri a Arewacin Nijeriya.