Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya baiwa Musulmi Nigeria Umarnin fara dubun watan Rabiyul Assani na shekara 1446.
“Gobe litinin shi ne 29 ga watan Rabiyul Awwal 1446 daidai da 22 ga watan Satumba 2025 ita ce Ranar da ya kamata al’ummar Musulmin Nigeria su fara duban jinjirin watan Rabiyul Assani”.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Shugaban Kwamitin ba da shawarwari Kan al’amuran da suka shafi harkokin addini na fadar Mai alfarma Sarkin Musulmi Farfesa Sambo wali Junaidu.

Sanarwar ta ce duk wanda ya ga jinjirin watan sai ya kai rahoton ga masaraken gargajiya dake kusa da shi domin Isar da sakon ga fadar Sarkin Musulmi .