Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta lura da wasu kalaman Barrister Abba Hikima, inda ya bayyana cewa hukumar ba ta da hurumin doka wajen sa baki a muhawarar da ke tsakanin Shehi Mai Tajul’izzi da Usman Maidubun Isa.
Hukumar tana bayyana cewa wannan matsayi da lauya Abba Hikima ya dauka ba daidai ba ne kuma yana nuna kuskuren fahimta kan dokokin da suka kafa hukumar a Jihar Kano.
Domin fayyacewa da kuma fadakar da jama’a, kan dalilin ta na saka baki kan muhawar mawakan ga wasu kamar haka:
1. Dukkansu Shehi Mai Tajul’izzi da Usman Maidubun Isa sha’irai ne da doka ta sakasu a karkashin kulawa da duba aikace-aikacensu gare mu.
2. Asalin abinda ya haifar da muhawarar da ta shiga tsakanin su ta samo asali ne daga kalaman waƙokinsu, wanda hakan ya sanya lamarin cikin ikon hukumar bisa tsarin dokarta.
Dokar da ta kafa Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta bai wa hukumar ikon da ya haɗa da:
1. Yin rajista da bayar da lasisi ga sha’irai.
2. Kula da abin da suke fitarwa (wakokinsu) da sa ido kan ayyukansu a bainar jama’a wato yayin majalisi.

3. Tabbatar da bin doka da oda, ciki har da bincike, hukunta masu karya doka, ko dakatar da lasisin su idan ya zama dole.
Saboda haka, hukumar tana da cikakken ikon doka wajen sa baki a irin wannan lamari, don kare zaman lafiya, tarbiyya da martabar bangaren masu yabon mazan Allah (S.A.W).
Kada Ka Rudar da Tarihi, Ba Ka Cikin Wadanda Suka Kafa APC – Alfindiki Ya Fadawa Kwankwaso
Mu na girmama ra’ayoyin masana a bangaren shari’a, tare da jan hankalisu kan cewa irin wannan kuskuren fassara daga masu ilmin doka musamman wadanda suka san tsarin doka irin shi Abba Hikima, na iya rage darajar hukumomin gwamnati.
A wata sanarwar da jami’in yada labaran hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya aikowa Kadaura24, ya ce Hukumar na kira ga duk masu ruwa da tsaki da su ci gaba da yin aiki cikin lumana da bin dokar hukumar yadda ya kamata.